Jump to content

Nafada

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nafada


Wuri
Map
 11°08′00″N 11°15′00″E / 11.1333°N 11.25°E / 11.1333; 11.25
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Gombe
Labarin ƙasa
Yawan fili 1,586 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Rafin Nafad
kauyen nafada
kauyen nafada

Nafada karamar hukuma[1] ce (LGA) a jihar Gombe[2], Najeriya . [3]Hedkwatarta tana cikin garin Nafada a gabashin yankin a11°05′44″N 11°19′58″E / 11.09556°N 11.33278°E / 11.09556; 11.33278, akan kogin Gongola wanda ya ratsa yankin. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar alif 2006, ƙaramar hukumar tana da faɗin murabba'in kilomita 1,586 kuma tana da yawan jama'a 138,185. Nafada tana da unguwanni goma (10) da suka haɗa da: Nafada East, Nafada ta tsakiya,Nafada ta yamma,Jigawa, Birin Fulani East, Birin Bolewa, Birin Fulani West, Gudukku, Barwo/Nasarawo da Barwo Windi.[4]

Nafada tana cikin yankunan gargajiya[5] a mutanen Bole. Ita ce babban birnin masarautar Gombe daga shekara ta alif 1913 zuwa shekara ta alif 1919. Masarautar Gombe ta koma Doma wadda daga baya ta koma Gombe.

Nafada na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi goma sha ɗaya (11) dake aiki a jihar Gombe a Najeriya. Tana da hedikwatar gudanarwa a garin Nafada kuma tana ƙarƙashin ƙananan hukumomin Gombe ta Arewa don haka ta zama mazabar tarayya da karamar hukumar Dukku.[6] Garine da suke son karatu[7] na addini[8], domin haka suna da yawan malaman addini da kuma alkalai. Suna amfani da harshen fillanci duk da sunada alaƙa da bolawa, amma fulfulde shine yaren da sukeyi cikin garin da ma ƙananan ƙauyukan da ke kewaye dasu.

Nafada itace iyakar gombe da kuma jihar yobe wato dai itace karshen gombe state.

Sarautar Gargajiya

[gyara sashe | gyara masomin]

Kamar kowace yanki a cikin Nigeria, nafada tana da masauratar ta wacce a rubutaccen tarihi tun shekarar 1581, tun kafin kafuwar jihar gombe.

A shekarar alif 2019, saidu Alkali shi ne senata mai wakiltar Gombe ta arewa Sai Kuma Aishatu jibiril Dukku[9] a matsayin Ɗan majalisa tarayya Mai wakiltar Dukku da Nafada. A shekarar alif 2020 Mai girman gwamnan jihar Gombe wato His excellency Alhaji Muhammad Inuwa Yahya ya daura Musa Abubakar babawuro a matsayin chairman din Nafada da mataimakinsa Salisu Shuaibu Dandele bi da bi. A ranar 15 ga watan Augusta Mai girma chairman din Nafada yayi hatsari har ya rasu.[10]

A shekara ta alif 2023, tsohon gwamnan Gombe wato his excellency Ibrahim Hassan dankwambo[11] shine ya dawo senata mai wakiltar Gombe ta arewa Wanda ya hada da Dukku,Nafada, Gombe, funakaye da kwami Kuma Abdullahi El-Rasheed a matsayin Dan majalisa Mai wakiltar Nafada da Dukku.[12]

Lambar gidan waya ta Nafada ita ce 762.[13]

Gundumar Sanata

Nafada

Nafada LGA belongs to Gombe North Senatorial Zone/District with Dukku, Funakaye, Kwami and Gombe LGAs

Mazabar Tarayya

Karamar hukumar Nafada na mazabar Nafada/Dukku ne wanda ya kunshi dukkanin yankunan:

  1. Karamar Hukumar Nafada
  2. Karamar Hukumar Dukku

Mazabu na tarayya a Najeriya sun kunshi rukunin kananan hukumomi ne a wata jiha kuma wani mai girma dan majalisar wakilai na tarayya ya wakilta.

Ƙaramar hukumar Nafada tana da yawan fili mai fadin murabba'in kilomita 1,586 kuma tana da matsakaicin zafin jiki 33. °C.

Kogin Gongola ya ratsa ta ƙaramar hukumar kuma yankin yana da matsakaicin yanayin zafi na kashi 20 cikin dari Kogin Nafada ya samo asali ne daga Kogin Gongola yana tasowa daga gangaren Gabas ta Jos-Plateau kuma ya fada cikin rafin Gongola da ke gudana daga arewa-maso-gabas har zuwa lokacin. Nafada sannan ya ci gaba da tafiya daya zuwa tafkin Chadi. A halin yanzu, ta juya kudu da kudu maso gabas har sai ta shiga kogin Hawal. Daga nan sai kogin ya bi ta kudu zuwa kogin Binuwai, ya hade shi daura da garin Numan. Babban kogin da kuma mafi yawan magudanan ruwa rafuffuka ne na yanayi waɗanda ke cika cikin sauri a watan Agusta da Satumba kowace shekara. Dam din Dadin Kowa da ke kusa da Gombe ya kame kasan kogin. Kiri Dam yana a karamar hukumar Shelleng ta jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya wanda aka gina don samar da ban ruwa ga Kamfanin Sugar na Savannah.

Yanayi (Climate)

[gyara sashe | gyara masomin]

Nafada, lokacin rani yana da zafi, wani ɓangare kuma gizagizai ne, yayin da lokacin damina ke tsananin zafi da gajimare. Matsakaicin zafin jiki na shekara-shekara ya tashi daga 60 zuwa 105 Fahrenheit, da wuya faɗuwa ƙasa da 55 ko tashi sama da 109.

  1. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.voahausa.com/amp/7509942.html&ved=2ahUKEwiWhOLG5fiGAxW-XEEAHeBoDzAQyM8BKAB6BAgKEAI&usg=AOvVaw32k9qQx0PGwFXW0V8VzE_d
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://aminiya.ng/an-kama-kansila-da-basarake-kan-satar-tiransfoma-a-gombe/&ved=2ahUKEwi9mIns5fiGAxVqTkEAHVCbC6YQxfQBKAB6BAgdEAE&usg=AOvVaw2GU_XRRinxp8rjh0DqSrhT
  3. https://tribuneonlineng.com/nafada-council-boss-killed-in-road-accident-gombe-gov-mourns/
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-12-25. Retrieved 2022-12-25.
  5. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.dw.com/ha/gidan-abincin-gargajiya-a-kano/video-66952188&ved=2ahUKEwiogfij5viGAxUGQEEAHXb1DhcQxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw3RbVh1IWQt1Uxtuk4TDuUM
  6. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-12-25. Retrieved 2022-12-25.
  7. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/c0ke7kz7kz2o.amp&ved=2ahUKEwjHhJ_t5viGAxUxaEEAHRhlBgkQyM8BKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw3lLntyo-4112LbOZH3LecH
  8. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/c0jjj5yk4wqo.amp&ved=2ahUKEwifoKOM5_iGAxUBWkEAHWQaBIYQyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw3npMNFJp0I16P_BH_L_gww
  9. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailytrust.com/aishatu-jibril-dukku-more-of-a-disciplinarian-than-pampering-mum/&ved=2ahUKEwjBoanX5_iGAxUvX0EAHcx0B1sQxfQBKAB6BAgOEAI&usg=AOvVaw28JM75sIRHvBOB5AezriiS
  10. https://leadership.ng/nafada-lg-chairman-dies-in-road-crash/
  11. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=http://guardian.ng/dankwambo-urges-national-assembly-to-support-buhari/&ved=2ahUKEwiykOGM6PiGAxW9W0EAHTF_CogQxfQBKAB6BAgVEAI&usg=AOvVaw18JYtpoGe0oM-x9uaAj02j
  12. https://dailytrust.com/ex-governor-dankwambo-unseats-senator-alkali-in-gombe/
  13. https://web.archive.org/web/20091007011423/http://www.nipost.gov.ng/PostCode.aspx

Samfuri:Gombe State