Jump to content

Annabi Ibrahim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Annabi Ibrahim
Annabawa a Musulunci


Saleh (en) Fassara - Lot in Islam (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Ur (en) Fassara da Babylonia (en) Fassara, 1810s "BCE"
Mutuwa Hebron (en) Fassara, unknown value
Ƴan uwa
Mahaifi Terah in Islam
Abokiyar zama Sarah (en) Fassara
Hajara
Yara
Ƴan uwa
Sana'a
Sana'a Mai da'awa da manzo
Muhimman ayyuka Binding of Ismail (en) Fassara
Scrolls of Abraham (en) Fassara

Bisa ga Imanin Addinin Musulunci, Annabi Ibrahim (Larabci: إِبْرَاهِيْمُ‎, romanized: ʾIbrāhīm, Arabic pronunciation: [ʔɪbraːˈhiːm]) Annabi ne kuma manzo Allah,[1][2] kuma Kaka ga Larabawa Isma'ilawa da Isra'ilawa.[1] Annabi Ibrahim ya bayar da babbar gudummuwa a matsayin misali na ban gaskiya cikin Yahudanci, Kiristanci, da Musulunci.[1]

A aƙidar musulmi, Annabi Ibrahim ya cika dukkan dokoki da jarabawowin da Allah (SWT) ya raya shi a tsawon rayuwarsa. A sakamakon ban gaskiyar da yake da ita ga Allah, Allah ya yi wa Annabi Ibrahim alkawari cewa zai zama shugaba ga dukan al’ummai na duniya.[3] Alkur'ani mai girma ya daukaka Annabi Ibrahim (AS) a matsayin abin koyi, mai biyayya ba mai bautar gumaka ba.[4]

A cikin wannan ma'ana, an kwatanta Annabi Ibrahim a matsayin wakiltar "mutum na farko a duniya ya mika wuya ga Haƙiƙanin Allahntaka kafin rarrabuwar ta zuwa addinan da suka rabu da juna ta hanyar bambance-bambancen tsari".[5] :18Musulmai sun yi imani da cewa Annabi Ibrahim da dansa Annabi Isma'il ne suka gina Ka'aba da ke garin Makka a matsayin gidan ibada na farko a duniya.

Ana gudanar da ranar Idin Al-Adha mai tsarki a Musulunci don tunawa da yadda Annabi Ibrahim ya sadaukar da dansa bisa umarnin Allah, da kuma karshen aikin hajji na Ka'aba.

Sadaukarwar Annabi Ibrahim

Musulmai sunyi imani cewa Annabi Ibrahim, wanda aka fi sani da Khalilullah (Larabci: خليل الله Trans: abokin Allah), ya zama shugaban salihai a zamaninsa kuma ta hanyarsa ne Adnaniyawa - Larabawa da Isra'ilawa suka zo. Ibrahim, a akidar Musulunci, ya bada gudummuwa kwarai da gaske wajen tsarkake duniya daga bautar gumaka a lokacin.

Annabi Ibrahim ya kawar da maguzanci a cikin ƙasashen Larabawa da mutanen Kan'ana. Ya tsarkake wurare biyu a ruhaniya tare da tsarkake gidajen ibada ta jiki. Annabi Ibrahim da Annabi Isma'il (Isma'il) sun kara kafa ayyukan hajji,[6] wanda har yanzu musulmai suke bi.

Musulmai sun yi iƙirarin cewa Annabi Ibrahim ya ƙara roƙi Allah ya albarkaci zuriyarsa, Annabi Isma'il da Annabi Is'haq (Ishak), kuma ya kiyaye zuriyarsa gaba ɗaya cikin tsarin Allah.

  1. 1.0 1.1 1.2 (Farhad ed.). Missing or empty |title= (help)
  2. [Al Kur'ani 87:19]
  3. [Al Kur'ani 2:124]
  4. [Al Kur'ani 16:120]
  5. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Glasse
  6. [Al Kur'ani 2:128]