Jump to content

Julia M. Riley

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Julia M. Riley (née Hill, an haife ta ne a shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da arba'in da bakwai (1947) ƙwararriya ce Kuma masaniyar ilmin taurari ce ƴar kasar Biritaniya wadda ta haɓaka rarrabuwar Fanaroff–Riley .

Bayanan sirri da na sana'a

[gyara sashe | gyara masomin]

Ita ce 'yar Philippa (wadda aka Haifa a Pass) kuma masaniyar ilimin kimiya na ruwa na Biritaniya Maurice Hill kuma jikanyar Nobel Prize - masaniyar ilimin kimiyar lissafi Archibald Vivian Hill.Riley ɗan'uwa ne na Kwalejin Girton mai alaƙa da Rukunin Astrophysics na Cavendish a Jami'ar Cambridge. Fannin bincikenta na farko shine a fannin ilimin taurarin rediyo . Riley tana karantar da laccoci kuma tana kula da ilimin kimiyyar lissafi a cikin Tripos na Kimiyyar Halitta a Jami'ar Cambridge.

Fanaroff-Riley nau'in I da II

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da huɗu (1974), tare da Bernard Fanaroff, ta rubuta takarda [1] ta rarraba taurarin radiyo zuwa nau'ikan halittar su (siffar su). Fanaroff da Riley's rarrabuwa zama aka sani da Fanaroff–Riley type I da II na rediyo galaxies (FRI da FRII). A cikin majiyoyin FRI babban ɓangaren watsawar rediyo yana zuwa daga kusa da tsakiyar tushen, yayin da a cikin majiyoyin FRII babban ɓangaren hayaƙin tana fitowa ne daga wurare masu zafi da ke nesa da cibiyar (duba tauraron dan adam mai aiki ).

  1. Empty citation (help)